A Aljeriya, yayin da wa’adin ajiye takardun neman takara a zaben neman shugabancin kasar ke kawo karshe da misalign karfe 12 na daren jiya Asabar 26 ga watan Oktoba, ‘yan takara hudu ne aka rawaito cewa sun aje takardun neman takara a zaben.

Tunda farko dai wadanda suka ajiya takardunsu ta neman tsayawa zaben, sun hada da tsohon ministan al’adu na kasarAzzedine Mihoubi, da kuma Abdelkader Bengrina na jam’iyyar islama.

Bayanai daga kasar sun ce da safiyar yau Asabar an samu kuma wasu ‘yan takara da suka aje takardunsu, da suka hada da Ali Zeghdud na karamar jam’iyyar (RA), sai kuma Abdelmajid Tebbune wanda shi ne firaministan kasar na farko ga shugaban kasar mai murabus Abdelaziz Buteflika, kafin daga bisani a sallame shi a shekara 2017.

Yanzu dai babbar ayar tambayar da ake azawa ita ce ta takarar Ali Benflis, tsaohon shugaban gwamnatin Bouteflika, wanda daga bisani ya kasance mai adawa da shugaba Buteflikan.

A ranar 12 ga watan Disamba ne aka tsara gudnar da zaben shugaban kasar ta Aljeriya, saidai har yanzu wasu jama’ar kasar na ci gaba da zanga zangar kin amincewa da zaben, wadanda suke ganin ba za’ayi adalici a ciki ba, kasancewar duk makusantan tsohon shugaban kasar mai murabus ne ke jen ragamar mulkin kasar.