Hukumar kwallon kafa ta AFrika, CAF, na ci gaba da matsin lamba ga Jamhuriya Kamaru akan ta gaggauta kammala ayyukan gina filayen kwallon kafa ta yadda za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar a shekara 2021.

Hukumar ta CAF na son Kamaru ta kammala ayyukan kafin nan da watan Yuni na 2020, kamar yadda sakataren hukumar Anthony Baffoe ya sanar, bayan kammala wani ran gadin gadi domin ganewa ido halin da ake ciki kan ayyukan a kasar ta Kamaru.

Tawagar hukumar ta CAF, na sanya ido ne kan yadda ayyukan ke tafiya a kasar ta Kamaru, inda za’a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na CHAN a 2020 da kuma ta kofin Afrika a 2021, sai dai a cewar tawagar har yanzu da sauran aiki a ga kasar ta Kamaru.

A bara ne hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta kwace damar da ta ba Kamaru ta daukar nauyin gasar cin kofin Afirka da ta gabata.

Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta samun jinkiri wajen kammala ayyuka a filayen wasan da za a yi amfani da su a lokacin gasar da za a yi a watan Yunin da ya gabata.