Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Afrika ta Kudu da Najeriya zasu baiwa ‘yan kasuwansu biza mai wa’adin shekara 10


Kasashen Najeriya da Afrika ta kudu, sun cimma wata yarjejeniya a tsakaninsu ta baiwa ‘yan kasuwan kasashen biyu da malaman makarantu takatar biza (visa) mai wa’adin shekara goma.

kasashen sun amince da hakan ne ne bayan kammala taron hukumar hadin gwiwa ta tsakaninsu karo na tara da ya gudana a Pretoria, wanda Shuwagabannin kasashen biyu, Muhammadu Buhari da takwaransa na Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa suka jagoranta.

Ministan harkokin wajen kasashen biyu ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.
An dai dauki matakin ne domin inganta alaka tsakanin al'ummomin kasashen biyu da habaka tattalin arzikinsu, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafafen yada labarai, Garba Shehu ya fitar.

Wannan dai na zuwa ne bayan hare-haren kin jinin baki da ya lakume rayukan ‘yan waje da dama a Afirka ta Kudu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu