Shugaba Trump, na Amurka, ya bayyana akwai sauren sojojin kasarsa kadan a Syria.

Kafin hakan dama sakataren tsaron Amurka, Mark Esper, ya ce dakarun kasar kimanin 1,000 da za a janye daga arewa maso gabashin Syria, za su koma yammacin kasar Iraki, domin taimakawa kasar, da kuma aikin yakar kungiyar IS

Batun janye sojojin na Amurka daga Syria, ya janwo zazzafar muhawara tsakanin manyan jami’an Amurka, inda ake ta sukan matakin.
Daga cikin masu sukar matakin na Trump, har da wasu makusantansa.

A makon da ya gabata ne, shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa dakarun Amurka za su bar Syria, amma kuma za su ci gaba da kasancewa a yankin gabas ta tsakiya domin bibiyar yanayin yankin, yayin da wani adadi kalilan na dakarun za su zauna a sansanin sojin na At Tanf dake kudancin Syria domin yaki da ragowar kungiyar IS.