Shugaban Majalisar zartarwa na kasar Yemen ya bayyana cewa Al'ummar kasar Yemen na da hakkin ci gaba da gwagwarmaya har zuwa lokacin da za su 'yanto kasarsu daga 'yan mamaya.

Shugaban majalisar zartarwa na kasar Yemen Mahdi al-Mashat cikin wani jawabi da ya gabatar a daren lahadi da ya gabata ya yi ishara kan gagaruwan nasarar da dakarun kasar suka samu a baya-bayan nan, tare da cewa ya kamata kawancen mamaya na Saudiya su sake tunani kan lissafin da suka yi a baya.

Al-Mashat ya jinjina wa al'ummar kasar kan irin goyon bayan da suke bawa Sojoji da dakarun sa kai na kasar tare da bayyana cewa hare-haren wuce gona da irin da kawancen Saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen da nufin mamaye kasar ba zai yi nasara ba.

Har ila yau shugaban Majalisar zartarwa na kasar Yemen ya yi kakkausar suka kan irin cikas din da kasar Saudiya ke kawo wa kan shawarar da aka gabatar na kawo karshen harin wuce gona da iri kan al'ummar kasar tare da neman kungiyoyin kasa da kasa su goyon bayan al'ummar kasar Yemen din da ake zalinta.