Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Imani da Allah madaukakin sarki da kuma kaunar Ahlul Bayti su ne su ka hada al’ummun Iran da Iraki.

A wani sako da aka wallafa a shafinTwitter na jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran; ya ci gaba da alaka zukatan al’ummun Iran da Iraki suna dunkule wuri guda saboda imani da kuma son iyalan gidan manzon tsira, da Imam Hussain Dan Ali.
Sanarwar ta jagoran ta zo ne a matsayin yin tsokaci dangane da abubuwan da suke faruwa a cikin kasar Iraki a bayan nan.
Ayatullah sayyid Ali Khamnei ya ci gaba da cewa; Karfin alakar kasashen biyu zai cigaba da bunkasa a kowace rana.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce; Kokarin da makiya suke yi na samar da Baraka a tsakanin Iran da Iraq, ba zai je ko’ina ba domin makircinsu zai ci kasa.