Ministan harkokin cikin gidan kasar Aljeriya ya karyata zargin da wasu mabiya addinin kirista na kasar suke yi wa mahukuntan kasar na rufe wasu daga cikin maji’iun mabiya addinin kirista.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya ska a shafinsa na yanar gizo a yau, Salahuddin Dahmun ministan harkokin cikin gida na kasar Aljeriya ya bayyana cewa, babu gaskiya a zargin da wasu mabiya addinin kirista na kasar suka yi ma ma’aikatarsa, akan rufe wasu daga cikin majami’unsu.

Ya ce wannan zargi wanda wasu daga cikin kiristoci mabiya darikar Protestant suka yi, ya yi hannu riga da abin da yake gaskiya, inda ya bayyana cewa ba su rufe wata majami’a a kasar ba.

Haka nan kuma minsitan ya yi ishara da cewa, akwai wasu matakai da aka dauka na dakatar da wasu daga cikin wuraren ibada a kasar saboda rashin cika ka’idoji wajen gina su, ko kuma aikata wasu abubuwa da ake shakku a kansu.

Ya kara da cewa, wannan matakin ya hada da masallatai na musulmi da kuma wasu majami’oi, wanda hakan ya hada da rashin samun izini wajen gina su, ta yadda ake ba su samar ad suka kamala takardun izini kafin ci gaba da yin amfani da wuraren, ko kuma ikata wasu abubuwa da ke jawo shakku, kamar wasu daga cikin wuraren da ake ganin suna kasha makudan kudade ba tare da an san daga ina kudaden suke shigo musu ba.