Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Alkarawi Ya Bukaci A Dage Lokacin Zabe A KasarTunisiaShugaban jam’iyyar “Qalb Tunis” na kasar Tunisia wanda a halin yanzu yake tsare a gidan kaso a babban birnin kasar, ya bukaci kwamitin zaben kasar ya dage zaben shugaban kasa zagaye na biyu wanda za’a gudanar a ranar lahadi mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli na kasar Turkiya ya nakalto Nabil Al-Qarawi yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa kwamitin zaben, ya kuma kara da cewa, a matsayinsa na wanda ya sami nasara a zaben shugaban kasa zagaye na farko wanda aka gudanar a ranar 17 ga watan Satumban day a gabata, yana bukatar zuwa larduna 24 na kasar, don zantawa kai tsaye da mutanen kasar kafin zabe zagaye na biyu.

A sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na farko wanda kwamitin zaben kasar ya bayyana, Nabil Alqarawi dan takarar jam’iyyar “Qalbu Tunis” da kuma Qais bin Sa’id na jam’iyyar Annahdha ne suka sami kuri’u mafi yawa, don haka su ne zasu tsaya a zabe zagaye na biyu wanda za’a gudanar a ranar 13 ga wannan watan da muke ciki.

A ranar 17 ga watan Nuwamba mai zuwa ne yakamata a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Tunisia, amma mutuwar shugaban kasar Qa’id Assibsi a cikin watan yuli ya sa aka gaggauta gudanar da zaben

Post a Comment

0 Comments

Close Menu