Kamfanin dillancin labaran kasar Faransaya habarta cewa ambaliyar ruwa ta mamaye kauyuka masu yawan gaske a kananan hukumomi 7 daga cikin 21 na jahar Adamawa.

Wannan Iftila’in na ambaliyar ruwa ya biyo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a makon da ya gabata.

Rahotani na daga jihar Adamawa dake arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa dubban mutane ne suka rasa muhallansu a sanadiyar ambaliyar, jami’an kai agaji sun bayyana ambaliyar ruwan a matsayin mafi muni da aka taba fuskanta a jihar Adamawa.