Shugaban Jam’iyar Ennahda ta tabbatar da samun nasara a zaben ‘yan majalisar dokoki na kasar Tununsiya.

Tashar talabijin din Aljazera mallakin kasar Aljazera ta nakalto Rached Ghannouchi shugaban jam’iyar Ennahda cikin wani taron manema labarai da ya gabatara wannan litinin, ya yi ishara kan sakamakon zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da ya wakana a ranar lahadin da ta gabata, inda ya tabbatar da samun nasarar jam’iyarsa ta Ennahda. 

Ghannouchi ya ce babu wani kokonto a game da samun nasarar da jam’iyar Ennahda ta samu azaben ‘yan Majalisar, don haka da zarar sun kafa gwamnati, zababbun al’ummar kasar za su mayar da hankali wajen yaki da ta ci hanci da rashawa da kuma samarwa matasan kasar aikin yi tare da ciyar da kasar gaba.

A jiya lahadi ne aka gudanar da zaben ‘yan Majalisar Dokoki karo na uku a kasar Tunusyiya tun bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi bn Ali a shekarar 2011.

Sakamakon farko da yake fitowa daga hukumar zaben kasar ta Tunusiya ya ce jam’iyar Ennahda c eke kan gaba, inda jami’iyar Kalbe Tunisiya ke biyarta a matsayi na biyu.

Hukumar zaben zaben kasar Tunusiya ta sanar da cewa a ranar laraba ce za ta fitar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.