Rahotanni daga Iran sun ce wani jirgin dankon man Iran din ya yi bindiga bayan tashin wani abin fashewa a kusa a gabar tekun Saudiyya da ke Jiddah.

Kafofin yada labaran Iran sun ce fashewar jirgin ta auku ne a tazarar kilomita 97 daga gabar.

Gobarar ta lalata manyan rumbunan mai biyu na jirgin ruwan mallakin kamfanin mai na kasar Iran (NIOC) da kuma tsiyayar mai a tekun Maliya.

Zuwa yanzu babu karin bayani kan ko akwai hasarar rayuka a gobarar jirgin mai suna Sabiti, kamar yadda kamfanin NIOC ya bayyana.

Wata kafar talabijin din Iran Al Alam ta ce an harbi jirgin ne da makamai masu linzami, amma kamfanin jiragen dakon mai na Iran (NITC) ya karyata zargin.