Gwamnatin kasar Amurka ta amincewa kasar Iraqi ta ci gaba da sayan iskar gas da kuma wutan lantarki daga kasar Iran na wasu watannu 4.

Wannan shi ne karo na 3 kenan wanda Amurka take toge kasar ta Iraqi daga takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasar Iraqi tana shigo da iskar gas daga kasar Iran ne don amfanin injinan bada wutan lantarki na kasar, wadanda suke samar da kasha har kashi 45 % na wutan lantarkin da kasar take amfani da shi mai yawan Magawatt 14,000.

Har’ila ila yau kasar Iran tana sayarwa kasar ta Iraqi wutan lanatarki magawatta 1000 guda kai tsaye.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya ce Gwamnatin Amurkan ta bukaci kasar Iraqi ta yi amfani da wannan damar don dogaro da kanta wajen samun makamashi da kanta ba tare da shigo da shi daga kasar Iran ba.

Tun bayan takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa Iran a shekara 2017 ne take daga kafa ga wasu kawayenta don sayan man fetur ko makamashi daga kasar Iran.

Da farko kasar Iraqi ta sami dagewar kafa na kwanaki 45, sai watanni 3 sannan yanzun kuma na watannin 4 daga watan yunin daya gabata.