Gwamnatin Amurka ta yi da’awar cewa an halaka shugaban kungiyar Daesh Abubakar Baghdadi a Syria.

Tashar Presstv ta bayar da rahoton cewa, jami’an ma’aikatar tsaron kasar Amurka Pentagon sun ce Abubakar Bagdadi ya halaka a wani hari da sojojin na Amurka suka kai a maboyarsa a garin Idlib da ke arewa maso gabashin kasar Syria.

Wani babban jami’in Pentagon ya sheda wa jaridar Newsweek ta kasar Amurka cewa, suna da tabbaci kan cewa harin nasu ya yi nasara wajen kashe Abubakar Bagdadi.
Sai dai wasu majiyoyin a ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka sun ce, Abubakar Bagdadi shi ne ya kashe kansa da kansa a lokacin da ake kai harin, inda ya saka wata jigidar bama-bamai kuma ya tarwatsa kansa, amma harin ya yi sanadiyyar mutuwar matansa biyu.

A yau ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai yi wani jawabi kan batun kisan Abubakar Bagdadi.