Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa ta amince da bukatar da gwamnatin Saudiyya ta gabatar mata, da ke neman Amurka ta kara ba ta kariya, ta hanyar aikewa da karin dubban sojoji zuwa kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya Juma’a sakataren tsaron kasar Amurka Mark Esper ya sanar da cewa, Amurka za ta kara aikewa da wasu karin dubban sojoji zuwa kasar Saudiyya, domin baiwa kasar kariya.
Sakataren tsaron kasar ta Amurka ya ce baya ga dubban sojoji, za su aike da karin wasu makaman kariya da za su girke a kasar, kamar yadda za su aike da jiragen sama na yaki.

A nasa bangaren shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, Saudiyya ta amince za ta biya dukkanin da Amurka ke bukata domin gudanar da wannan aiki na ba ta kariya.

Wannan mataki dai na zuwa bayan wasu daruruwan biliyoyin dalolin da Amurka ta karba daga kasar Saudiyya ne a cikin kasa da shekaru biyu da suka gabata, da sunan bai wa kasar ta Saudiyya kariya daga abin da Amurka take kira barazanar Iran.
Amma bayan kai harin da mayakan kasar Yemen suka yi kan babban kamfanin mai na Saudiyya, da kuma kame dubban sojojin Saudiyya da mayakan an Yemen suka yi, wannan yasa kasar ta Saudiyya ta kara kulla wata yarjejeniyar da Amurka duk da sunan neman kariya, inda za ta sake biyan wasu daruruwan biliyoyin dalolin ga gwamnatin Trump.