Ma’aikatar harkokin wajen Amurkace ta fitar da wannan sanarwar da aciki take bayyana cewa za ta bada ladan kudi sama da dala miliyan 5 ga duk wanda ya tsegumta bayanan da za su taimaka wajen gano wadanda suka kai harin kwantan bauna kan sojojinta guda 4 dake kasar Niger shekaru biyu da suka gabata musamman Adnan Abu Walid Alsharawi jagoran kungiyar ISIL dake da alaka da kungiyar Ta’ada dake kai hare hare ayankin sahara.

Harin kwantar baunar da aka kai a watan Oktoban shekara ta 2017 a kauyen Tongo Tango dake kudu masu yammacin kasar Niger ya janyo kashe sojojin Amurka 4.

Dake aikin tabbatar da zaman lafiya cikin dakarun hadin guiwa da sojojin kasar Niger, a lokacin da suke kokari kama wasu yan ta’adda. Kimanin sojojin kasar Niger guda 5 ne aka kashe a lokacin harin.