Hukumomin a Iraki, sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar kwanaki biyu bayan zanga zangar da aka kwashe kwanaki anayi a kasar.

Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan kawo karshen zanga zangar wacce a yayin ta mutane sama da dari suka rasa rayukansu, kana wasu dubbai suka jikkata.

Firaministan kasar Adel Abdel Mahdi, ya sha alwashin gudanar da abincike mai zurfi kan lamarin da kuma biyan diyya ga iyalen wadanda suka mutu a lamarin da suka hada da bangaren masu zanga zanga da kuma jami’an tsaro.

Mista Al-Mahdi a cikin jawabin da ya gabatar a jiya ya kuma sha alwashin duba jerin bukatun masu zanga zangar data sabo asali ta shafukan sada zumunta, kana kuma zai mika wa majalisar dokoin kasar bukatar neman gyaren fuska wa majalisar ministocin kasar.

Har kawo yanzu dai wasu bangarorin al’umma a kasar na ci gaba da kiraye kirayen firaministan kasar ya yi murabu daga mukaminsa.