A jiya Laraba ce majalisar Zartarwa a Nigeria ta amince da batun fara aiki da fara biyan mafi karanci albashi kamar yadda aka cimma matsaya a yarjejniyar da aka rattaba hannu tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago ta kasa NLC a makon jiya. Har ila yau majalisar ta bada umarnin a biya dukkan kudaden aryas- ariyasda maikatada ke bin gwamnati tun daga 18 ga watan Aprilu , kafin nan da 31 ga watan Decembar mai kamawa.

A wajen taron da aka gudanar a fadar shugaban kasar ministan kwadago na kasa Christ Ngige ya bayyana cewa an riga an cimma matsaya game da fara biyan mafi karancin albashi na N30,000, kana ya zayyana sunayen hukumomin gwamnati da matakin albashinsu.

Idan ana iya tuwana tun a watan Aprilun wannan shekarar ne shugaban Muhammadu Buhari ya sanya hannu a sabon tsarin biyan mafi karancin albashin, amma aka yi ta kai ruwa rana tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago game da fara aiki da shi, musamman game kan karin albashin wasu maaikata dake wasu matakai na albashin.