A safiyar Jiya jumma’a ce aka bude taron shuwagabannin kungiyar kasashe yan baruwammu (NAM) karo na 18 a birnin Baku babban birnin kasar Azebaijan.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya bayyana cewa shugaban kasar Venezuela Nicola Madorus ne ya bude taron da jawabinsa.

Kafin haka dai ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar 120 sun gudanar da taron kwanaki biyu, don sherawa shuwagabannin kasashensu taron na yau jumma’a da kuma gobe Asabar.

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani yana daga cikin shuwagabannin kasashen kungiyar da suke halattan taron na Baku.

Kuma ana saran nan gaba zai gabatar da jawabi a taron, inda zai bayyana ra’ayin kasar Iran kan matsalolin yankin da kuma duniya gaba daya.