Firaministan kasar Mali, Boubou Cisse, ya kaddamar da shirin kwance damarar makamai a yankin Mopti dake tsakiyar kasar a wani mataki na shinfada zaman lafiya a yankin.

Shirin wanda ake kira (DDR), ya kunshi karbar makamai manya da kananansu daga hannun ‘yan bindiga da ‘yan tawaye kuma shigar dasu aikin soji.

Mahukuntan na Mali, sun bayyana mahimmancin shirin, wanda a cewarsu zai ragewa ko kuma kawo karshen mallakar duk wani irin makami.

Shirin na da manufar shinfida zaman lafiya mai daurewa a yankin da ya jima yana fuskantar matsalar ‘yan tada kayar baya.

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali, MUNISMA, na daga cikin masu hann da shuni da suka tallafawa shirin, wanda yake da gurin karbar makamai dake hannun jama’a ba bisa ka’iba ba, inda ake fatan mutane 8,500 ne shirin zai shafa a jihohin da suka hada da Mopti da kuma Segu.