A yau Lahadi 27-10-2019 ne a ka gudanar da tinawa ranar Shahadar Manzon Allah (s.a.w.a) 

Daruruwan yan'uwa Almajiran Sayyid Zakzaky ne suka zo  daga warare daban daban sun halarci taron Zikira na tinawa da shahadar Manzon (S.A.W.A) markaz a nan garin kaduna,  inda suka karanta ziyarori da addu'o'i na musamman don zagayowan wannan ranar. Sannan mawaka sun yi ta rera wakokin Jimami ga Manzon Allah, da sauran Shuhada. 

Sanna Sayyid Jawad ya gudanar da jawabi na musamman, yayi bayani akan wafatin manzon Allah (S .A .W .A) da irin jarabawowin da ya fuskanta kafin wafatin sa.

Bayan kammala jawabin na sa, Malam Aliyu bakin ruwa ya yi takaice cen Karin haske, game da musa'ib din gidan Ahliy Muhammad da wadan da suka biyo bayan su (koyi da su).
San ya rufe jawabin nasa da ziyarar Ma'aiki (S).


Manzon Allah (S) yayi Shahada ne 28 Ga watan Safar a Madina Shekara ta goma Bayan hijira. 

Kaduna Press a madadin Da'irar kaduna. Muna yiwa al-ummar musulmi musamman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah.(s) Ta'aziyar zagayowan wannan ranar. Ta Shahadar Manzon Allah (S)