An kai hari kan wani masallaci a birnin Bayn da ke yammacin kasar Faransa.

Kaduna Press ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sputnik cewa, a jiya Litinin wani mutum dan kimanin shekaru 70 da haihuwa ya bude wutar bindiga  akan wani masallaci a garon Bayon na kasar Faransa.

Rahotanni sun ce akalla mutane biyu ne suka jikkata sakamakon kai wannan hari, daya daga cikin mutanen yana cikin mawuyacin hali.

Jami’an ‘yan sandan kasar Faransa sun ce sun cafke mutumin da ya kai harin, kuma sun yi kira ga mutane da su karacewa wurin da aka kai harin.

Babu wani Karin haske da jami’an ‘yan sanda na kasar Faransa suka bayar kan dalilin kai wannan hari a kan masallacin musulmi a garin na Bayon, amma dai sun ce suna cikin gudanar da bincike.