An jiyo karan fashewar abubuwa guda biyu wadanda ake kyautata zaton harin makamai masu linzami ne kan wani jirgin dakon man fetur na Iran, a kusa da tashar ruwan birnin Jeddah na Saudiyya.

Harin dai ya faru da sanyin safiyar yau Juma’a, kan wani jirgin kamfanin man fetur na kasar Iran (NIOC), wanda ya lalata tankar mai guda biyu na jirgin.

Lamarin ya haddasa malalar man fetur a tekun yankin.

Tuni aka fara kaddamar da bincike kan lamarin, a yayin da kwararu ke ganin cewa harin ta’addanci ne.

Babu wanda ya rasa ransa a lamarin a yayin da ake ta kokarin kashe gobarar.
Ku kasance tare da Kaduna Press dan
Karin bayanni