‘Yan sandan Birtaniya sun kai samame a wasu wurare biyu a yankin Ireland ta arewa, a neman masu alaka da gawawwakin mutane 39 da aka samu a cikin wata motar daukar kaya.

A Jiya Laraba neaka sanar da samun gawawwakin mutane 38 da wani matashi guda a cikin wata babbar mota a yankin masana’antu, mai nisan kilo mita 20 daga tsakiyar birnin London.

‘Yan sandan sun kame matukin motar dan shekaru 25 wanda ya fito daga yankin Ireland ta arewa, bisa zarginsa da ake yi da kisan kai.

Sanarwar da ‘yan sandan su ka fitar ta ambaci cewa; Motar daukar kayan ta isa Essex a kudancin Ingila, ta kuma taso ne daga Zeebrugge daga kasar Belgium. An sami gawawwakin mutane 39 a cikin motar da ake dangantawa da fasakwaurin mutane.

Firmaministan kasar Birtaniya Johnson ya bayyana damuwarsa akan abinda ya faru sannan kuma yana karbar rahoto akan halin da ake ciki a kowace rana.