Shugaban kasar Benin, Patrice Talon, ya kira wani taron kwanaki uku domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin siyasa a kasar.

Taron da za’a fara a ranar 10 ga watan Oktoban nan zai hada dukkan jam’iyyun siyasa na kasar amma wadanda suka cika sabbin sharuddan kafa jam’iyyun siyasa a kasar.

Taron na zuwa ne bayan rikicin da ya biyo bayan zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na ranar 28 ga watan Afrilu da ya gabata inda aka hana dukkan jam’iyyun adawa na kasar tsayawa takara.

Bayanai daga kasar sun ce shugaban Talon, ya gayyaci jam’iyyun siyasa tara, wadanda kawai suka cika sabbin sharuddan kafa jam’iyyun siyasa a kasar.

Sai dai jam’iyyun adawan da aka gayyata sun gindaya sharudda da dama kafin su shiga taron.

Daga cikinsu kuwa har da ta tsohon shugaban kasar Boni Yayi, amma ban da ta hamshakan dan kasuwan nan Sebastien Ajavon wanda aka hukunta ba tare da ya halarci zaman kotu ba.