A Labanon, an shiga kwana na hudu a zanga zangar da jama’ar kasar ke yi kan a abunda suka danganta da cin hanci da rashawa da son kai da ya mamaye ‘yan siyasar kasar.

Rahotanni daga kasar sun ce ko a jiya Lahadi ma ‘yan kasar maza da mata sun nufi tsakiyar Beyrouth, babban birnin kasar a ci gaba da neman ‘yan siyasar su yi murabus.

Zanga zangar dai ta samo asali ne daga sanya haraji da gwamnatin kasar kan kira ta hanyar manhajar watsapp.
Duk da cewa gwamnatin kasar ta janye matakin daga bisani, amma hakan bai hana boren ba.

Tuni dai jam’iyyar (FL), ta Kristoci dake mara wa firaministan kasar Saad Hariri baya ta sanar da murabus din ministocinta guda hudu, saboda a cewarta gwamnatin ba zata iya shawo kan matsalar ba.

A yau Litini ne wa’adin kwanaki uku da firaministan Hariri, ya dibarwa gwamnatinsa na ta dubi bukatunsa ke kawo karshe.