Rahotani daga Tunisia na cewa, an sallami dan takarar shugaban kasar Nabil Karawidaga gidan yarin Monarguia inda ake tsare da shi.

A jiya ne wata kotun kasar ta yanke hukuncin sallamar Mista Nabil Karawi, wanda ya yi takara shugabancin kasar yana tsare a gidan yari, ya kuma zo na biyu a zaben.

Tun a ranar 23 ga watan Agusta ne ake tsare da dan takaran Nabil Karawi, bisa zargin kaucewa biyan kudaden haraji da halasta kudaden haramu.

Matakin kotun na sallamar dan takaran Nabil Karawi, na zuwa ne a yayin da ya rage kwanaki hudu a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda zai fafata da dan takaran da ya zo na farko a zaben zagayen farko,Kais Sa’ed, wanda a makon da ya gabata ya dakatar da yakin neman zabensa, domin nuna adalci ga abokin hammmayarsa dake garkame a gidan yari