Hukumomin jihar Kaduna a Najeriya, sun ce an sako daliban nan mata shida da kuma malaman makarantar nan biyu na kwalejin Engravers da aka sace makwanni uku da suka gabata, kamar yadda mai Magana da yayun gwamnan jihar Samuel Aruwan ya sanar.

Tuni dai a cewarsa aka damka daliban ga iyayensu, saidai babu karin bayyani na ko an biya kudin fansa kafin a sako mutanen ko kuma a’a.

A baya bayan nan matsalar garkuwa da mutane na dada kamari a arewacin wannan kasar ta Najeriya, musamman a jihohin Zamfara da kuam Kaduna.

A ranar 4 ga watan Oktoba, gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya sanar da cewa wadanda sukayi garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa.