Gwamnatoci da masu hannu da shuni da ‘yan manyan ‘yan kasuwa duniya, da suka yi taro a birnin Lyon na Faransa sun yi alkawarin bayar da gudunmuwar Dala Biliyan 14 don yaki da cututukan da suka hada da AIDS/SIDA da zazzabin cizon sauro ko malaria da kuma tarin-fuka A duniya.

Ana fatan wadanan kudaden za su taimaka wajen ceton rayukan mutane akalla miliyan 16 daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2023.

Shugaban asusun ajiyar kudaden, Peter Sands ya ce, suna sa ran nan da shekarar 2023 su rage yawan mace-macen da cutar AIDS da Malaria da tarin-fuka ke haddasawa da akalla rabi.

Haka zalika ana sa ran kare mutane miliyan 234 daga kamuwa da cututtukan.

Tarin-Fuka da AIDS sun kashe mutane kimanin miliyan 1.7 a shekarar 2017, yayin da Malaria ta hallaka sama da mutane dubu 430, kuma mafi yawansu a nahiyar Afrika.