Minitsan man fetur na Iran Bijan Zanganeh ya bayyana cewa ya gana da takwarana na kasar Saudiyya a birnin Moscow na kasar Rasha Zanganeh ya ce; Na shaida masa cewa mu abokai ne na tsawon shekaru 22; duk da cewa an alakar ta fuskanci fadi tashi, don haka babu wata matsala idan an sake haduwa.

Zanganeh ya kara da cewa; Ba Iran ce ta fara haddasa rashin jituwa da Saudiyyar ba, kuma ita kasa ce da take son bunkasa alaka da dukkanin kasashen wannan yankin.”

Ministan man fetur din na Iran ya kuma ce; Bai kamata saudiyyar ta dauki Iran a matsayin abokiyar gaba ba, ya kamata su sani abokan gaba su ne wadanda su ka shigo cikin wannan yankin daga waje.

Har ila yau, ministan man fetru din na Iran ya ce; ya gana da dukkanin takwarorinsa na kasashen kungiya masu arzikin iskar gas da suke taro a birnin Moscow na kasar Rasha.