A Burkina faso, daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zangar kyammar ayyukan ta’addanci da kuma la’antar ci gaba da kasancewar sojojin ketare a nahiyar Afrika.

An gudanar da zanga zanagr ce bisa kiran wasu gomman kungiyoyin fara hula kan abunda suka danganta da mamaya.
Masu zanga zangar na raira taken ‘’sojojin Faransa ba ma so a Burkina faso, sojojin ketare ba ma so a Afrika’’.

Ayyukan ta’addanci a cewar kakakin gamayar kungiyoyin fara hular, Gabin Korbéogo, sun kasance a wannan zamani wani salo da ake amfani dashi don girge sojojin kasashen ketare, da suka hada da sojojin Faransa, Amurka, Canada, Jamus da dai saurensu, saidai duk da kasancewar wadanan sojojojin manyan kasashen duniya a yankin, kungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da cin karensu babu babbaka, fiye da yadda ake tsammani.

Yau sama da shekaru hudu kenan da Kasar Burkina faso dake yankin sahel, ke fuskantar ayyukan ta’addanci da ake dangantawa dana mayakan dake ikirari da sunan jihadi, masu alaka da kungiyoyin Al-Qaida da kuma IS.

Ko a jiya Juma’a ma mutane 16 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai kan wani masallaci a kusa da garin Gorom-Gorom dake arewacin kasar.