Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Zabi Firayi Ministan Habasha A Cikin Wadanda Suka Cancanci Kyautar Nobel Ta Wannan Shekara


Firai Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed na daga cikin wadanda aka zaba don samun kyautar Nobel ta wannan shekara ta 2019.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a ranar Jumma’an da ta gabata ce aka rubuta sunan Abiy Ahmed a cikin jerin mutanen da za su karbi wannan kyautar a wannan shekarar bayan wata yarinya diyar shekara 16 mai rajin kare yanayi wacce ake kira Greta Thunder.

Firai ministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed ya sami yabo daga kasashen duniya da dama bayan nasarar da ya samu kawo karshen zaman tankiya da yaki tsakanin kasarsa da kuma makobciyar ta kasar Eritrea a shekara da ta gabata.

Kasashen biyu sun shiga yaki a tsakaninsu na kimani shekaru 20 kafin Ahmed ya sami nasarar kawo karshen zaman tankiyar a shekara ta 2018 da ta gabata.

Banda haka firai ministan na Habasha ya taimaka wajen sasanta sojojin kasar Sudan da kuma shuwagabannin kungiyoyin fararen hula na kasar, sasantawar da ta kai ga kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar ta sudan daga karshe

Post a Comment

0 Comments

Close Menu