Kungiyoyin kare hakin bil-adama sun sanar da ci gaban rikici a arewacin kasar Tchadi.
Gidan radion kasa da kasa na kasar Faransa ya nakalto kungiyoyin kare hakin bil-adama na kasar Tchadi bayan wani taron hadin gwiwa da suka yi, sun fitar da sanarwar cewa har ya zuwa yanzu ana ci gaba da fada da makamai a yankin Tibesti na arewacin kasar tare kuma da nuna damuwarsu kan yadda ake ci gaba da kashe fararen hula a yankin.

A nata bangare, gwamnatin kasar Tchadi ta karyata duk wani labari da ake watsawa kan rikicin yankin na Tibesti tare da gargadin yada duk wani labari da ya shafi yankin.

Tun a tsakiyar makon da ya gabata ce rikici ya barke tsakanin Sojojin gwamnatin Tchadi da mutanan yankin dake kokarin kare kansu a yankinTibesti mai arzikin zinari.

Molly Sougui tsohon gwamnan yankin, ya fadawa radion kasa da kasa ta kasar Faransa cewa tun bayan da aka gano zinari a yankin, wasu matasa dake aikin hako da zinarin sukadauki makakamai da kuma kafa kungiya ta kare kansu daga duk wani farmaki daga bangaren dakarun gwamnatin kasar, to saidai a halin da ake ciki, gwamnati ta tura dakarun tsaro masu yawa domin hana hakar zinari a yankin, lamarin da ya yi sanadiyar musayar wuta tsakanin matasan yankin da dakarun tsaron gwamnati, tare da salwanta rayukan mutane masu yawa.

Sougui ya kara da cewa ma’aikatar tsaron kasar ta boye wannan labari ne da nufin kare rayukan mutane da kuma tabbatar da tsaro a yankin tare kuma da hana ci gaba da safarar ma’adinan karkashin kasa ta hanyar da ba ta dace ba.

Rahotani dake fitowa daga kasar Tchadi sun tabbatar da cewa akwai duban mutane dake yin gina domin neman zunari a kasa