Da yanmacin yau Laraba 30/10/2019, dai dai da 2 gawatan Rabi'ul Auwal, ne da'irar kaduna ta gudanar da sa tutar Muhammad rasulullah.

Kamar yadda a ka saba duk shekara ana saka tutar ne a husainiyya baqiyatullah, ne, a ranar daya ga watan Rabi'ul Auwal.

In mai karatu bai manta ba gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta afkawa jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da Almajiransa ne a ranar daya ga watan Rabi'ul Auwal a ranar 12-12-2015. 

Karkashin shugaban sojojin Najeriya Yusuf tukur Burtai, yadda ta kash sama da dubu, da kama sama da dubu.

Wakilin yan uwa na kaduna Malam Aliyu Tirmiz ne ya jagoranci saka tutar. Malam Aliyu ya yi jawabi game da sa tutar Muhammad rasulullah, in ya bayyana cewa: wanna saka tutar koyi ne da maulan mu Sayyid Zakzaky, da kuma tabbatar wa azzalumai cewa ko Malam bayanan a cikin mu abin da ya yi na saka tutar Manzon Allah, wanda ya zama laifi, to mu ma zamu cigaba da yin wannan laifin.

Sannan ya kara da cewa: mu mabiya gidan Manzon (S) muna da lokaci biyu na farin cikin da na bakin ciki, duk wani masyin Manzon Allah dole ne ya taya manzo (S) bakin ciki, idan lokacin bakin cikin da ta'addanci da akayi wa Manzon Allah (S) da iyalan gidansa, haka in na farin cikin ya zo.
Malam ya bayyana cewa hakki ne ga duk wani musulmi ya fito ya taya Manzon Allah farin ciki.


Karda mu cika ku da suru tu ga Audio nan kasa