Dakarta mai kula da shashen nahiyar Afirka a karkashin Asusunbayar da lamuni ( IMF) Mr. Abebe Selassie ne ya bayyana wannan matsayin a yayin taron shekara-shekara na asusun lamunin a birnin Washington na kasar Amurka.

Mr. Selassie yana amsa tambaya ne akan ko matakin da Najeriyar ta dauka na rufe iyakokinta na kasa da kasashen makwabta yana cin karo da yarjejeniyar cinikayya ta bai daya a tsakanin kasashen nahiyar ta Afirka.

Jami’in Asusun bada lamunin na kasa da kasa ya kara da cewa; Abinda mu ka fahimta shi ne cewa rufe iyakokin yana nufin magance fasa kwaurin kayan masarufi ne da aka dade ana yi.

Selassie ya kara da cewa; lamarin ya shafi harkar fasa kwauri ne da babu wanda zai so ace yana taimakawa.

Sai dai jami’in na bankin ba da lamuni na duniyar ya yi fatan ganin an shawo kan lamarin ta hanyar tattaunawa.