Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi kira ga kasashen nahiyar, da su karfafa hadin gwiwa a kan iyakokinsu wajen hana yaduwar kwayar cutar Ebola.

Kungiyar, ta hanyar hukumar hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC), ta bukaci karfafa hadin gwiwa a kan iyakokin juna game da riga kafi da matakan mayar da martani kan cutar Ebola tsakanin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo, yankin da cutar ta fi shafa da kasashen dake makwabtaka da ita, wanda a cewarta zai taimaka wajen hana yaduwar cutar zuwa sassan nahiyar.

hukumar ta CDC, ta sanar da cewa, za ta shirya wata ganawar ministocin lafiya na DRC da na kasashe 9 dake makwabtaka da ita, don tattauna matakan hadin gwiwa a kan iyakokin juna kan yaki da cutar ta Ebola.

Hukumar ta bayyana cewa, za a gudanar da wannan ganawa ce a ranar 21 ga watan Oktoba a Goma, babban birnin lardin arewacin Kivu na Jamhuriyar demokiradiyar Congo, an shirya taron ne bisa hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya.

A cewar AU, taron ministocin, zai kuma tattauna yadda za a aiwatar da hadin gwiwa a kan iyakokin kasashen, da yadda za a shirya da ma tuntukar barkewar kwayar cutar ta Ebola.