"Mutanen da ku ka ganmu da su, wanda hakan ke ba ku tsoro, to ba bindiga muka sa muka tattaro su ba, kuma ba mu buqatar Bindigar! …Rana daya ba ka da ikon ka (zo ka) ce abin da yake da tarihin shekara sama da Talatin da hudu wai bindiga ne ba! To mu yi mene da Bindiga? Tuntuni ba mu yi anfani da ita ba, (sai) yanzu ne muke da buqata?

"Yawan mutanen da kuke gani (a Harkar nan), har abin yake damun ku, ba da Bindiga muka tara su ba, ko mun dauki bindiga ne muka hahharbi mutane sai suka zozzo? Kira muka yi, mun sa hankali ne da ilimi, muka yi magana ta ilimi da hikima ga mutane, sai mutanen suka sa hankalinsu suka auna suka fahimta, shi ya sa suka zo, ba da makami muka tara su ba!"

— Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), daga littafin ZANTUKAN HIKIMA.