Latsa hoton bda ke sama don sauraron hirar Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar da Mukhtar Bawa na BBC Hausa:
Wani mai cibiyar ladabtarwa da aka fi sani da gidan mari ya sallami dukkan dalibansa, ya kuma rufe gidan da ke birnin Kano.
Hakan na zuwa ne bayan dirar mikiyar da 'yan sanda ke yi a kan gidajen marin da ake tsare "kangararru" a wasu sassa na kasar.
Sai dai Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar mai makarantar mari a Unguwar Arzai a Kano ya ce shi ba tsoron kar hukuma ta kama shi da laifi ne ya sa ya rufe gidan ba, don shi "ya yi amannar ba ya muzgunawa ko azabtar da wadanda yake kula da su".
Ko a karshen makon jiya, sai da hukumomi suka sake kai samame wani gidan mari da ke yankin Rigasa a cikin jihar Kaduna, inda suka kubutar da daurarru fiye da 100 ciki har da mata.
Gwamnatin Najeriya ta umarci 'yan sanda su rufe irin wadannan gidajen mari, da ake zargin ana cin zarafin daurarrun, a wasu lokuta ma har da zargin yin lalata.