Rahotanni dake fitowa daga kasar Bangaladesh sun bayyana cewa kimanin mutane 4 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu guda 50 suka jikkata bayan da ‘yan sanda suka bude wuta kan masu Zanga- zangar nuna rashin amincewa da wasu kalaman batanci ga manzon Allah tsira da aminci su tabbata gareshi da alayensa, da wani mutumin dan kasar Indiya yayi a shafinsa na fecebook.

Rahoton ya ci gaba da cewa a ranar Asabar da ta gabata ce aka kama wani mutumin kasar Indiya da ake zargi da yada wasu kalaman nuna batanci ga fiyayyen halitta Annabi Mohammad tsira da aminci su tabbata gareshi da alayensa, a shafinsa na fecebook, zargin da ya karyata , inda ya nuna cewa an yi masa kutse ne acikin shafin nasa. “Yan sanda sun kama mutane 3 da ake zargin suna da hannu wajen yin kutse a shafinsa na facebook.

Kasar Bangaladash dai ita ce kasa ta 9 a duniya a yawan musulmi, inda kashi 89% na alummar kasar musulmi ne yayin da kashi 9% kuma mabiya addinin Hindu ne