Babban bankin duniya ya sanar da shirinsa na zuba kudade da za su haura dala miliyan dari biyar domin habbaka yankin Chadi.

Wannan sanarwa dai ta zo ne a taron da bankin yake gudana a birnin Washington na kasar Amurka, wanda kuam ministar kudi ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmadda ke halartar taron ce ta sanar da hakan.

Bisa ga sanarwar dai, bankin zai bayar da tsabar kudi da za su aki dala miliyan 510, wadanda za a yi amfani da su a bangarori daban-daban da su sjafi farfado da yankin tafkin Chadi.

Daga cikin muhimamn abubuwan da za a yi da kudin akwai batun inganta tsaro a yankin, da kuma batun kwararowar Hamada wadda ke barazana ga makomar yankin, haka nan kuma za a ware wani bangaren kudi domin taimaka ma jama’ar yankin, da kuma inganta rayuwarsu.

Wadannan kudade za a kashe su ga al’ummomin kasashen yankin wadanda suke kewaye da tafkin Chadi, da suka hada da Nijar, Najeriya, Chadi da kuma Kamaru.