Kwamitin harkokin kasuwanci na Bankin Duniya (DB) ya sanya Najeriya cikin kasashe 20 a duniya wadanda suka sami ci gaban a zo a gani a bangaren inganta harkokin kasuwanci a kasashensu daga kasashe 190 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran Nigeriya NAN ya nakalto mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan lamuran tattalin arziki Dr Jumoke Oduwole tana fadar haka a Abuja.

Oduwole ta kara da cewa a ranar 24 ga watan Obtoba da muka shiga ne bankin duniya zai bayyana rahotonta na shekare-shekara kan harkokin kasuwanci a duniya, kuma tuni sun sami labarin cewa Najeriya na daga cikin kasashen suke sami ci gaba a harkokin kasuwanci musamman a bangaren kasuwancin ta na’urar sadarwa ta internt.

Oduwole ta kara da cewa kwamitin ya gudanar da bincikensa na harkokin kasuwanci a biranin Lagos da kuma Kano a tarayyar ta Nigeria, kafin ya fitar da wannan sakamakon.

Daga cikin cim gaban da aka samu dai, akwai maida harkokin a tashar jiragen ruwa na Lagos ya zama ta na’ira mai kwakwalwa, wanda ya sawwaka ayyuka, hakam hukumar custom da na shige da fishe, da wacce take rigistan kamfan