Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta da masaniya dangane da baraka a cikin kungiyar ASUU


Gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta da wata masaniya dangane da batun bullar baraka a cikin kungiyar malaman jami’o’in kasar ta ASUU.

Ma’aikatar ilimin kasar ta Najeriya wacce ta bayyana hakan a jiya, ta kuma ci gaba da cewa; Idan har ta tabbata an sami bullar baraka a kungiyar malaman ta ASUU, to, za ta zama ‘yar ba ruwanmu ba tare da goyon bayan wani bangare ba.

Mataimakin babban daraktan watsa labaru na ma’aikatar ilimi ta kasar Najeriya Bem Goong ne ya shaidawa jaridar Vanguard ta kasar wannan labari
Kungiyar wacce ta yi shekaru 41 da kafuwa, ta sami baraka inda aka sanar da kafa wata sabuwar kungiyar mai sunan; Majalisar Malaman Jami’a, ko kuma Congress Of University Academics wato ( CONUA) a takaice.

A shekaran jiya Asabar ne dai aka sanar da kafa sabuwar kungiyar a garin Ile-Ife a jahar Osun

KNPRSCD 08
Kaduna Press
Safuwan Harun✍🏼

Post a Comment

0 Comments

Close Menu