Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Buhari Ya Jaddada Bukatar Daukar Matakai Kan Kalaman Nuna Kiyayya A Najeriya


A jawabinsa na bukin cika shekaru 59 da samun ‘yencin kan kasa daga hannun turawan Ingila a shekara 1960, shugaban Muhammadu Buhari na tarayyarNajeriya ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace don kawo karshen kalamai masu bayyana kiyayya tsakanin al’ummar Najeriya.

Dangane da harkokin tsaro kuwa, shugaban ya yaba tare da jinijnawa jami’an tsaron kasar musamman sojoji da suka taka rawar gani wajen kyautata harkokin tsaron kasar zuwa inda yake a halin yanzu.

Shugaban ya kara da cewa a kokarin gwamnatinsa na kyautata harkokin tsaro, a halin yanzun shirye-shirye sun kammala don daukar Karin ‘yansanda har dubu 10.
Har ila yau shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa tayi wa ma’aikatar yansandar kasar garan bawul don kara kyautata ayyukansu.

Ko bayan ga hakan Shugaba Buhariya tabobatunkula da yankin Niger Dalter, hadin kan kasar, dogaro da wasu hanyoyin samun kudade wadanda ba man fetur ba, da kuma jagoranci na gari a kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu