Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta’addanci da wasu amsu da’awar jihadi suka kai a arewacin kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a Lahadi da ya gabata, wasu gungun mutane dauke muggan makamai da ake sa ran masu da’awar jihadi ne, sun isa kauyen Pobe-Mengao da ke tazarar kilo mita 200 daga arewacin birnin Wagadugu fadar mulkin kasar.

Rahoton ya ce, da farko ‘yan ta’addan sun yi barzanar cewa za su kame matasan kauyen su tafi da su, kuma suna bukatar mutanen kauyen su taimaka musu da kudi domin kara sayen makamai, a lokacin da mutanen kauyen suka ki amincewa da hakan, nan take suka bude wuta a kansu, kuma suka kashe mutane akalla 16 kamar dai yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

Kasar Burkina Faso dai ta fara fuskantar barazanar ayyukan ‘yan ta’adda ne tun kiman shekaru biyar da suka gabata, inda ‘yan ta’addan suke barazana ga yankunan arewacin kasar da ke kusa da iyaka da Mali.