Akalla mutane 16 suka rasa rayukansu sannan wasu biyu na daban suka jikkata a wani farmaki da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan wani Masallaci a arewacin kasar Burkina Faso.

Hukumomin tsaro a kasar sun ce, maharan sun afkawa masu ibadar ne a babban masallacin garin Salmossi da misalin karfe 7 zuwa 8 na daren Juma’ar da ta gabata , inda suka bude musu wuta.

Duk da cewa kasar Burkina Faso na daga cikin kasashen Afrika masu fama da hare-haren ta’addanci, mafi akasarin ‘yan kasar na adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare a kasar, musamman na Faransa da ta yi musu mulkin mallaka.

A ranar asabar da ta gabata, kimanin mutane dubu 1 suka yi zanga-zanga a Ouagadougou, babban birnin kasar, don yin tir da ta’addanci da kuma kafa sansanonin sojojin kasashen Turai da Amurka a nahiyar Afrika.