Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf sanar da cewa sun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun zabe ta jihar Kano ta yanke da ke tabbatar da Abdullahi Ganduje amatsayin zababben gwamnan kano.

Abbab Kabir Yusuf ya bayyana cewa tuni lauyoyinsu suka daukaka kara zuwa kotun Kaduna, kuma akwai manayan lauyoyi da sza su bi kadun shari’ar.

Mai shari’ar Halima Shamaki ce ta yanke hukunci a jiya Laraba a shari’ar da ake yi ta zaben gwamnan jihar Kano, inda ta ce Abdullahi Ganduje ne zababben gwamnan jihar, saboda babu wasu dalilai da aka gabatar da ta gasu das u da ke tabbatar da cewa an yi magudi a zaben na Kano.

Zaben an gwamnan jihar Kano dai shi ne zaben da yafi daukar hankula a lokacin zaben ranar 23 ga watan Maris, wanda hukumar zabe ta dakatar fadin sakamakonsa biyo bayan hatsaniyar da aka samu a lokacin da ake gab da kammala shi a wasu mazabu, wanda aka ida kammalawa daga bisani.