Dr. Hassan Rauhani wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Tehran a jiya Litinin ya kara da cewa; A jinyan za mu iya bugun kirji mu fadi cewa; makirce-makircen da Amurka, da masu girman kai na duniya, ‘yan sahayoniya, da ‘yan korensu a wannan yankin suka kitsawa Iran, ya zo karshe.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Su kansu makiya Iran sun yi furuci da cewa dauriya da aiki da hankali da tsayin daka da jajurcewa sun taka rawa wajen fitar da Iran daga halin da aka shigar da ita ciki.

Wani sashe na jawabin shugagan kasar ta Iran ya tabo kokarin da gwamnatinsa take yi na bunkasa tattalin arzikin kasar duk da matsin lamba ta koli da take fuskanta.

Da ya koma Magana akan tattalin arba’in da ake yi zuwa Iraki, shugaban kasar ta Iran ya jinjinawa al’ummar Iraki saboda yadda suke karbar baki, haka nan dukkanin kungiyoyi da bangarori na al’umma da suke taka rawa.

Shugaban kasar na Iran yabayyana matsayar Iran akan harin da Turkiya take kai wa a kasar Syria, yana mai yin kira ga gwamnatin Ankara da ta kawo karshen hare-haren nata.

Akan shiga tsakanin da Pakistan take tsakanin Iran da Saudiyya shugaba Hassan Rauhani ya ce; Piraminstan kasar Pakistan Zai Isar Da mahangarmu Ga Saudiyya.