Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

EFCC Tana Hana Satar Naira Biliyan 4.5 A Kowane WataHukumar fada da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta ce; A kowane wata tana tseratar da kudaden da suka dai Naira Biliyan 4.5 daga ma’aikatan bogi

A wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar ta EFCC ta fitar, Mr. Wilson Uwujaren yanakalto shugaban hukumar Ibrahim Magu yana cewa; ya zuwa yanzu sun hana salwantar Naira Biliyan 54 da ake sacewa da sunan ma’aikatan bogi.

Magu ya gabatar da jawabi ne wanda kakakin hukumar ya wakilce shi, a kwalejin tsaro ta kasa dake birnin Abuja, a jiya Alhamis wanda ya dauki taken; “Cin Hanci Da Rashawa Da Dabarun Fada Da Shi A Najeriya.”

Magu ya jaddada aniyar wannan gwamnatin na fada da cin hanci da rahsaw a cikin kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu