A jawabinsa na farko bayan da dakarun kasarsa suka fara kai farmaki a kasar Siriya, Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan yayi da’awar cewa Dakarun kasar suna fada da ta’addanci ne a kasar Siriya.

Shugaba Erdogan ya ce wannan farmaki da sojin kasar suka fara kaiwa siriya zai magance barzanar tsaro ta ciki da wajen kasar, domin haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki wannan mataki na kawo karshen ‘yan ta’adda a duk inda suke.
Ba tare da yayi ishara da wata kasa ba, Shugaba Erdogan ya ce wadancan sun samar da ‘yan ta’adda ISIS a kan iyakan kasar, kuma sun samar da kungiyar YPG, suna baiwa ‘yan ta’adda makamai, kuma suna tsamanin kasar Turkiya za ta saurari maganarsu.

Yayin da ya koma kan kasashen da suke sukan matakin da kasarsa ta dauka, musaman ma kasar Saudiya, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa kamata ya yi mahukuntan kasar Saudiya su diba kansu a madibi, su waye suka jefa kasar Yemen cikin wannan mawuyacin hali, tare da kashe duban mutane?

A bangare guda kuma shugaban kasar ta Turkiya ya soki gwamnatin kasar Masar, inda shugaban kasar Masar ba shi da bakin Magana a kan wannan saboda ya kashe tafarkin Dimokadiya a kasar Masar.

Yayin da ya koma kan kasashen Turai, Shugaba Erdogan ya ce idan kasashen Turai suna tunanin cewa aikin da muke yi kama karya ne, to za babu matsala, za mu bude hanya ga ‘yan gudun hijra miliyan 3 da dubu 600 zuwa kasashen na Turai.