A matsayin mayar da martani na nuna adawa da hare-haren da gwamnatin birnin Ankara ta kai kaiwa kan arewacin Siriya, gwamnatin Faransa ta dakatar da sayarwa kasar ta Turkiya makamai.

Cikin wani jawabin hadin gwiwa da suka fitar a daren jiya asabar, ma’aikatun harakokin waje da na Tsaron Faransa sun sanar da cewa daga jiya asabar gwamnatin Faransa ta dakatar da sayarwa kasar Turkiya makamai a matsayin mayar da martani na nuna adawa da hare-haren da take kaiwa arewacin kasar Siriya, tare da bayana cewa hakan na barazana ga harakokin tsaron kasashen Turai.

Kafin hakan dai kasashen Finland da Norway da Holland gami daJamus sun dakakar da sayarwa kasar ta Turkiya makamai domin nuna rashin amncewarsu da yadda gwamnatin kasar take kai hare-hare arewacin kasar ta Siriya.

Manyan kasashen Turan sun dauki matakin ne, bayan da dubban mutane a kasashen na Faransa da Jamus, suka gudanar da zanga-zangar adawa da hare-haren dakarun Turkiya kan mayakan Kurdawa a arewacin Syria.

Wadanda suka shirya zanga-zangar, sun ce sama da mutane dubu 20 ne suka fita gangamin a birnin Paris, yayinda a birnin Cologne a Jamus, sama da mutane dubu 10 suka shiga zanga-zangar.

Ranar laraba, 9 ga watan Oktoba, 2019, dakarun Turkiya suka kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG a arewacin Syria, wadanda Turkiyan ke kallo a matsayin yan ta’adda, kuma reshen haramtacciyar jam’iyyar Kurdawan kasar da ta dauki makamai domin kafa kasa mai cin gashin kanta.