A Zimbabwe, giwaye 55 ne aka rawaito cewa kishirwa da yunwa sun kashe sakamakon fari dake kara muni a kasar.

Da yake sanar da hakan ga manema labarai, kakakin wuraren da ake killace namun dajin kasar ya ce an gano gawarwakin giwaye da dama a gewayen wuraren da dama da ruwa ya kafe a kasar.

Wani kwararre ya bayyana cewa, ko baya ga rashin ruwa, habakar al’umma na tilastawa giwaye da dama nisantar wuraren da ake killace su domin neman abunda za su ci, kuma a cikin irin wannan tafiyar ce dayawa daga cikinsu ke mutuwa.

Ko baya ga hakan wasu na ganin cewa, rashin ware kasafin kudi mai tsoka na kula da dabbobin daga gwamnati na taimakawa wajen batansu, inda wasu ke ganin mafita guda ce illa a sayar da dabbobin ga wuraren ajiye namun daji na kasashen waje.

Sai dai masu rajin kare namun daji, na korafi akan irin wannan shawarar wacce suke ganin ana raba giwaye da danginsu a tura su gidajen namun wadanda ba su dace ba kamar a kasar China.